Alfarma Na Yi Wa Kwankwaso Na Bar Shi Ya Yi Takara A 1999- Ganduje

271

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya karɓi Rabi’u Sulaiman-Bichi, tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kano da ‘yan tawagarsa da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Idan dai za a iya tunawa, jim kaɗan bayan da Kotun Ƙoli ta ba Gwamna Ganduje nasara ranar Litinin, Mista Sulaiman-Bichi ya bayyana aniyarsa ta barin tsohon abokinsa a siyasance, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Amma, majiyoyin dake kusa da tsohon Shugaban Jam’iyyar sun ce ya so ya bar jam’iyyar tun kafin hukuncin na Kotun Ƙoli.

“Hukuncin Rabi’u Sulaiman Bichi ba shi da alaƙa da hukuncin Kotun Ƙoli. Ya ɗauki matakin ne bisa aƙidu da dalilan ƙashin kai”, a cewar wani abokin siyasarsa na kusa, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa.

Da yake karɓar Mista Sulaiman-Bichi da sauran jagororin Kwankwasiyya daga ƙananan hukumomi 44 a Fadar Gwamnatin Jihar Kano ranar Alhamis, Gwamna Ganduje ya yabe su bisa ta maza da suka yi na ‘yanta kansu daga abinda ya kira “ɗariƙar Kwankwasiyya mai son kai”.

Ya ce: “Ko a shekarar 1999 lokacin da gwamnatin soja ta ɗage hanin kan al’amuran siyasa, mun gudanar da zaɓen fitar da gwani a PDP, kuma waɗanda suka shiga wannan zaɓe sun sani cewa ni ne, Abdullahi Umar Ganduje na yi nasara, amma aka canza alƙaluma don a daɗaɗa masa.

“A lokacin na ce ban yadda ba a sake sabon zaɓen fitar da gwani. Amma aka shawarce ni in haƙura da cewa a sake zaɓe don a samu zaman lafiya. Na haƙura, na bar abin haka.

“Na yadda da zuciya ɗaya. Lokacin da ya yi ƙoƙarin ya nuna min cewa ya yi min alfarma ne bisa yin haka, na faɗa masa gaba da gaba cewa ba alfarma ya yi min na zama mataimakinsa ba a takara.

“Na fahimtar da shi cewa abinda nake buƙata kuma nake sha’awa shi ne a sake wani sabon zaɓen fitar da gwani. Ku tambaye shi me ya faru tsakanina da shi. Dattawa irin su Alhaji Lili Gabari su suka ƙara haƙurƙurtar da ni”, in ji Gwamna Ganduje.

A nasa ɓangaren, Mista Sulaiman-Bichi ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa APC ne don amsa kiran da Gwamna Ganduje ya yi wa abokan hamayya na su zo su haɗu kai da shi don ciyar da jihar Kano gaba.

“Mun amince da irin jajircewar Gwmana Abdullahi Umar Ganduje na ciyar da jiharmu gaba, shi yasa lokacin da ya yi kira ga dukkan ‘yan hamayya da su zo su haɗa kai da shi wajen ciyar da jihar nan gaba, muka yanke shawarar mu zo mu bada gudunmawa don ciyar da jihar gaba”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan