Home / Siyasa / Da Atiku Ne Shugaban Ƙasa Babu Shakka Zai Fi Buhari Ƙokari – Obasanjo

Da Atiku Ne Shugaban Ƙasa Babu Shakka Zai Fi Buhari Ƙokari – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa da al’ummar ƙasar nan sun zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa a zaben 2019 da ya fi shugaban kasa Muhammadu Buhari kokari duba da halin da kasar nan take ciki a yanzu.

Obasanjo ya bayyana haka ne yayin hira da aka yi da shi a gidan rediyon BBC sashen Yarbanci inda yace tabbas Atiku Abubakar sai ya fi Buhari kokari da kwatanta gaskiya a matsayin shugaban kasa.

“Abin da nake cewa a nan shi ne duba da halin da muke ciki a yau, idan ka dubi wadanda suke mulki a yau, har da ma shugaban namu gaba daya, na tabbata da Atiku Abubakar ne a mukamin da sai ya fi tabukawa.

“Atiku fa ba mala’ika bane, ya yi ma mutane da dama laifi, cikinsu har da ni kaina, amma kuma ya nemi gafara na, kuma na gafarta masa saboda koyarwar addini na, a matsayina na kirista, Ubangijina Yace na gafarta ma wanda ya yi min laifi, kuma abinda na yi kenan.

“Don haka lokacin da yazo wajena da malaman addinin kirista da islama yana rokon na gafarta masa, sai na ki gafarta masa, ni ubangiji ne? ba wai ina nufin halayensa na baya masu kyau bane, amma dukkanmi ajizai ne, ko akwai wanda bashi da laifi, idan akwai ya fito mu gan shi.” Inji shi.

Daga karshe Obasanjo ya nanata jawabinsa na cewa idan aka duba halin da ƙasar nan take ciki a yau, tabbas Atiku Abubakar sai ya fi kokari fiye da shugaban kasar yanzu, idan da shi ne ya samu irin wannan dama.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Rugujewar Kwankwasiyya ta kunno kai a jihar Kano – Fa’izu Alfindiki

Fitaccen mai adawa da tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *