Za A Bayar Da Kyautar Danƙareren Gidan Zama Ga Duk Mutumin Da Ya Ƙara Aure

10085

A kokarin da ta ke na rage yawan mata marasa aure, gwamnatin Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa za ta fara bayar da tallafin gidan zama ga duk mazan da suka auri mata 2.


Ministan Cigaba da Samar da Kayan More Rayuwa na Kasar Dakta Abdullah Belhaif Al-Nuaimi ne ya sanar da hakan a yayin zaman Majalisar Zartarwa na ranar Larabar nan inda ya ce, Ma’aikatarsa ta yanke wannan hukunci na bayar da taimakon gida ga masu mata biyu a kasar.


Ya ce, za a bayar da tallafin karkashin shirin samar da gidaje na Shaikh Zayed.


Ministan ya ce, gwamnati za ta samar wa da matar ta 2 komai kamar yadda ta farko ta ke da shi.


Gwamnatin kasar dai ta ce, bayar da wannan tallafi na gidan zama zai rage yawan mata marasa aure a kasar.

Turawa Abokai

6 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan