Auren Mace Fiye Da Ɗaya Shi Ne Silar Talaucin Mutanen Arewa – Sarki Sanusi II

255

Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II, ya bayyana cewa matukar mutanen yankin Arewa ba su canja al’adunsu ba to za su cigaba da zama a cikin bakin talauci ne da ci baya.

Sarkin ya yi wannan maganar ne a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a lokacin da ya halarci taron kaddamar da wata takarda da aka sanyawa suna ”Gudummawar makarantun jami’a wajen cigaban kasa’, wanda Dr Usman Bugaji ya gabatar a jami’ar tarayya ta garin Gusau a jiya Juma’a.

Sarkin ya bayyana cewa al’adar Hausa ta auren mace fiye da daya, bayan dayar ma ba iya daukar dawainiyar ta suke yi ba, shine babban musabbabin da ya sanya yankin arewa zai cigaba da zama a cikin rashin cigaba da talauci.

Ya ce: “Akwai mutanen da basa iya ciyar da mace daya ma, amma sai kaga sunje sun karo mata uku, sannan suyi ta haifar yaran da baza su iya daukar nauyinsu ba.”

Ya ce har sai mun canja wannan al’adar ta mu tukunna yankin arewa zai samu cigaba.

A cewar shi, “Yankin arewa na da kashi 80 na talauci, kudu kuma suna da kashi 20, saboda kawai mun dauki al’adar auren mata da yawa da haifar yaran da baza mu iya daukar nauyinsu ba, a karshe sai dai mu bar su suna bara a tituna.”

Ya kara da cewa wasu mazajen za su saki matansu, su tare yara masu yawan gaske, matan ne za su cigaba da daukar nauyinsu, Sarkin ya ce wannan kawai na daya daga cikin dalilan da ya sanya muke samun ‘yan ta’adda a yankin mu.

“Matsalar shaye-shaye, Boko Haram, ta’addanci da rashin aikin yi da muke fama dasu a yanzu, ba komai bane akan abinda zai zo mana nan da shekara 20 zuwa 30,” inji shi.

Ya bukaci jami’o’in Najeriya da su fito da wata hanya da za ta kawo karshen wannan al’ada ta mu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan