Ganduje Zai Yi Nadama A Ƙarshen Zangon Mulkin Sa – Kwankwaso

313

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso yace Gwamna mai ci Abdullahi Ganduje da mukarraban sa za suyi nadama lokacin da suka kawo karshen mulkin Jihar Kano.


Kwankwaso ya bayyana haka lokacin da yake wata hira a kafofin yada labaran Kano da suka yada kai tsaye, Kwankwaso yayi zargin cewar Gwamnatin Ganduje banda yaudara da karya babu abinda take shukawa mutanen Kano.


Sanata Kwankwaso yace a karshen mulkin Ganduje zai ce yayi nadama, da ya mikawa wanda ya lashe zaben da akayi a shekarar 2019.

Wadannan kalamai na Kwankwaso kamar mayar da martani ne ga kalaman Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ya bayyana shi a matsayin wanda ke kokarin sauya sheka zuwa APC domin takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023.


Yayin da yake karbar tsohon shugaban PDP Dakta Rabi’u Usman Bichi da ya sauya sheka zuwa APC, Gwamna Ganduje ya bayyana Kwankwaso a matsayin mai tsananin son kan sa da kuma kin yabawa da rawar da wasu ke takawa.


Ganduje yace yafi kowa sanin wanene Kwankwaso da kuma dabarun siyasar sa tare da kuma yadda yake zama da jama’a kana da kin yabawa wadanda suka bada gudumawa.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan