Minti Biyar Kacal Na Ke Ɗauka A Wajen Yin Kwalliya – Amina Mohammed

227

Amina J Mohammed, mataimakiyar Sakare Janar na Majlisar Dinkin Duniya, ta bayyana wasu abubuwa game da rayuwarta.

Cikin wata tattaunawa da gidan sashen Hausa na BBC, Amina Mohammed ta bayyana irin abincin da ta fi so a rayuwarta.

“Na fi son sakwara da miyar taushe a cikin abinci”

Da kuma aka tambaye ta game da tsawon lokacin da take dauka tana yin kwalliya, sai ta ce “jan baki kawai nake sakawa, sai kuma kwalli, minti biyar kawai na ke yi”

A cikin shekarar 2016 ne Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nada Ministar muhalli, Amina Mohammed a matsayin mataimakiyarsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan