Za A Kafa Ƙungiyar Tsaro Mai Laƙabin ‘Shege Ka Fasa’ A Arewacin Najeriya

280

A matsayin koyi da ƙungiyar tsaro ta yanki da aka haramta kwanan nan da gwamnonin Kudu Maso Gabashin Najeriya suka ƙirƙira mai suna Amotekun, Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa, CNG, ta yanke shawarar ƙirƙirar ƙungiyar tsaro mai suna ‘Shege ka Fasa’ da nufin shawo kan matsalar tsaro dake addabar yankin.

A cikin wata sanarwa da CNG ta fitar ranar Asabar, Mai Magana da Yawunta, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce kafa wannan ƙungiyar tsaro ya zama wajibi sakamakon gazawa a fili da gwamnati ta yi wajen sauke nauyin dake kanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa gaba ɗaya,

A cewar CNG, Shege ka Fasa za ta zama wani ƙarin matakin kare kai a yankin Arewacin Najeriya mai fama da ƙalubalen tsaro.

CNG ta ce: “A halin da ake ciki, Arewa ce ya kamata ta fi yin fushi bisa yadda kai wa al’ummarta hare-hare, ake lalata garuruwa da ƙauyuka, ake yin garkuwa da waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, waɗanda suka haɗa da yara, ake koya musu ta’addanci, ake zaluntar iyalai ,ake raba al’ummomi da matsugunansu a kullum.

“A dukkan wannan, Arewa ta kasance a cikin wani yanayin mai haɗari wanda wasu daga waje suka haifar, su waɗannan mutanen sun dogara ne da kawo irin waɗannan muggan makamai da muggan ƙwayoyi da sauran abubuwa masu cutarwa da kuma bazuwar makamai a yankin.

“Da wannan matakin fusata da damuwa da ake ciki a halin yanzu, da kuma rashin tabbas wanda ke rura wutar rikici da rashin girma juna tsakanin al’umma, CNG ta yi amanna cewa akwai buƙatar Arewa ta ɗauki matakai irin na gwamnonin Kudu Yammacin Najeriya don kare yankin da al’ummar yankin daga waɗannan hare-hare da ɓarna da ake yi kullum.

“Saboda haka, gazawar hukumomi wajen muna cewa lallai za su iya kare al’umma a dukkan sassan Arewa a matsayin hujja mafi ƙanƙanta da za ta nuna cewa da gaske suke yi game da nauyin da yake kansu, zai sa ya zama mutane ba su da wani zaɓi illa kafa ƙungiyar tsaro ta Arewa Security Initiative mai laƙabin Shege ka Fasa don kare rayukan al’ummarsu”, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan