Hukuncin Kisa Ga Maryam Sanda Cigaba Ne Ga Ɓangaren Shari’a – Dr Mansur Sokoto

1906

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan na jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto, Dakta Mansur Ibrahim Sokoto, ya bayyana hukuncin da mai shari’a Halilu Yusuf, na babbar kotun Abuja, akan Maryam Sanda a matsayin cigaba a bangaren shari’ar ƙasar nan.

Dakta Mansur Sokoto ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na fasebuk, jim kadan da yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

“hukuncin kisa ga Maryam Sanda ci gaba ne ga sashen Shari’a. Hukuncin Allah ke nan. Tausaya wa mai laifi ga hukuncin Allah laifi ne”

Tun da farko dai ana tuhumar Maryam Sanda da kashe mijinta, Bilyaminu Bello Halliru, ta hanyar daba masa wuka da sauran makamai masu hatsari.

Idan za a iya tunawa dai tun a cikin watan Nuwambar shekarar 2017 aka gurfanar da Maryam Sanda, bisa zargin kashe mijinta, Bilyaminu Bello Halliru.

Mutuwar Bilyaminu Bello Halliru, wanda da ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Bello Halliru ta ja hankalin mutane da dama shafukan sada zumunta a fadin ƙasar nan.

Turawa Abokai

1 Sako

 1. Bawai munki da hukunci da Allah yace a yineba
  Ammah anyone amfanida son zuciya wajen yin shari’ar saboda da shi ne yakashe ta
  Baza’a yanke masa wanna hukuncin ba
  Saboda baban sa wanine a Nigerian
  Soboda subawasu bane a kasar
  Mutun nawa suke kashe mutane a kasar Nan ammah ba’a taba kashe wani ko wata sai eta saboda suba wasubane a kasar

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan