Baƙin Jinin Kofa Ne Ya Kayar Da Shi Zaɓe – Abdullahi Abbas

103

Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya bayyana cewa sunyi duk wani kokari domin ganin Hon Kofa ya koma kan kujerarshi amma abin yaci tura bisa rashin zabarshi da jama’ar yankin sukaki yi.

“Mun yi duk abinda zamu iya da mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Ganduje, duk da alaka mai tsami tsakaninmu, mun shiga garuruwan Bebeji da Kiru don neman mutane su zabeshi.”

“Hakan ne dalilin da yasa ya samu wasu kuri’un da ya samu a zaben da aka kammala, ina tabbatar maku cewar mutanen yankin basa sonshi shiyasa suka hanashi komawa.”

Ya kuma kara da cewa, Honarabul Abdulmuminu Jibrin ne ya kayar da kanshi Amma jam’iyyar APC tayi iya iyawar ta

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan