Eriksen Na Gab da Shiga Inter Milan

238

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta bayar da tabbacin cewa Christian Eriksen na dab da shiga kungiyar.

Domin a jiya Litinin dan wasan yaje can kasar ta Italia inda aka gwada l lafiyarsa kuma aka tabbatar lafiyarsa lau.

Tun abaya kungiyoyin kwallon kafa da dama suka nuna sha’awarsu ta daukan wannan dan wasan amma hakansa bai cimma ruwa ba.

Shima haka Eriksen tun abaya ya kwallafawa ransa cewar yanason zuwa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid shima hakansa bai cimma ruwa ba.

Tun a wasannin baya masana akan harkar wasanni da magoya bayan Tottenham na duniya harda ma na nan gida Najeriya suka bayar da tabbacin cewar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fita daga ran Eriksen duba da salon wasannin dayake bugawa ba kamar na can baya ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan