Ƴan Sanda Sun Damƙe Wani Matashi Ɗauke Da Gawar Almajiri A Cikin Buhu

494

Al’ummar unguwar Dorayi karama da ke yankin ƙaramar hukumar Dala, a jihar Kano, sun cafke wani mutum mai suna Musa da ya jefar da gawar wani almajiri mai suna Nasir a yankin.

Al’amarin ya faru ne da yammacin yau Laraba, inda wata mata mai suna Amina ta hangoshi ta katanga a yayin da ya jefar da gawar, sannan yayi mata barazanar cewa zai kashe ta.

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar mana da cewar, sun ga gawar an rufe ta a cikin wani abu, da alama kuma har ta fara canja kamar ta, kuma ganin basu amince da abun da aka jefar ba ya sanya suka yi tara da tara suka damke mutumin nan take.

Rahotonni daga unguwar na cewa wanda aka kashe wani almajiri ne mai suna Nasiru, yau tsawon kwanaki biyar kenan malamin sa na neman sa.


Kazalika al’ummar unguwar sun bayyana cewa ‘yan sanda sun cafke matashin da ya jefar da gawar da kuma uwar dakin almajirin.


Sai dai har kawo haɗa wannan rahoton bamu samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ba, sai dai zuwa nan gaba in mun samu zamu sanar daku.

Dala FM, Kano

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan