NYSC Ta Ƙara Alawus Na Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Zuwa N33,000- DG

208

Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya yi ƙarin haske game da adadin da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi a matsayin alawus-alawus na Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima, wanda zai yi daidai da sabon Mafi Ƙarancin Albashi na Ƙasa.

Ya Bayyana haka ne yayinda yake yi wa Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima jawabi a Sakatariyar NYSC ta Jihar Bauchi a yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar.

Mista Ibrahim ya ce saɓanin alƙaluma daban-daban da ake bayarwa a Soshiyal Midiya, tabbatacciyar magana ita an amince da N33,000 ne a matsayin sabon alawus.

Ya kuma ce na yi tanadin biyan sabon alawus ɗin a Kasafin Kuɗin 2020, yana mai ƙarawa da cewa NYSC za ta fara biyan wannan sabon alawus da zarar hukumomin da abin ya shafa sun saki kuɗaɗen.

Ya kuma shawarci Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima da su zamo masu kaffa-kaffa da harkar tsaro, su guji yaɗa jita-jita da kuma yin amfani da Soshiyal Midiya ba yadda ya dace ba.

Ya gargaɗe su su guji yin tafiye-tafiye ba tare da izini ba, idan kuma an ba su izinin yin tafiya, kar su yi tafiyar dare, saboda haɗarin dake tattare da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan