Ƙasar Nan Tana Cikin Halin Yaƙi A Yanzu – Fadar Shugaban Ƙasa

315

Fadar shugaban ƙasar nan ta ce abin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari bai yi sauyin manyan hafsoshin tsaron kasar ba shi ne, saboda kasar nan ta na cikin halin yaki.

Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da BBC a ranar Alhamis.

Kakakin shugaban kasar na martani ne ga masu kira da a sauya manyan hafsoshin tsaron kasar da suka shafe shekaru suna jagoranci, abin da ba kasafai aka saba gani ba.

Kazalika maganganunsa martani ne ga shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan kasar Sanata Eyinnaya Abaribe, da ya nemi shugaban ya yi murabus saboda gaza shawo kan matsalar tsaro a zaman majalisar na ranar Laraba.

Garba Shehu ya ce “duk masu kushe ko suka kan manyan jami’an tsaron nan ba sa la’akari da cewa ko an ki ko an so Najeriya a cikin halin yaki take a yanzu.

“A matsayin Shugaba Buhari na tsohon janar a soja, yana sane da lokacin da ya kamata ya yi canjin kwamandoji da kuma lokacin da bai kamata ba.”

Sannan mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, Najeriya ta samu kanta a wannan hali ne tun bayan fantsamar kungiyar IS wadda ta faro daga Iraki da Syria, da kuma rikicin Libiya.

“Amma abin lura shi ne kowa ya san cewa Shugaba Buhari na bakin kokarinsa don kare rayuwa da dukiyar ‘yan kasar nan tamu.”

Daga cikin masu sukar gwamnatin game da gaza shawo kan matsalar tsaro har da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, da ke cewa matsalolin da al’ummar kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro a yanzu ba ya rasa nasaba da yadda gwamnati ke tafi da mulki.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan