Na Yiwa Rabi’u Kwankwaso Ritaya A Siyasa – Ganduje

807

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen cike gurbin da ya gabata a matsayin hujja mai ƙarfi da ya ke nuna cewa ya yiwa tsohon mai gidansa ritaya a siyasa.

Ganduje ya bayyana cewar ya yiwa Sanata Rabi’u Kwankwaso ritaya a siyasa ganin yadda ƴan jam iyyar APC ne ke da nasara a zaɓen da ya gabata.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da shugaban majalisar dokokin jihar Kano ke gabatar da ƴan takarar majalisar da suka yi nasara a zaɓen da ya gabata, Ganduje ya ce lissafin siyasa ne ya kai ga matakin da yake kai a yanzu.

Ya ce a yanzu jam iyyar APC ce ke mulki tun daga sama har ƙasa, kuma tsarin da yake da shi ne ya sa shi matsayin da yake a a yanzu.

Turawa Abokai

2 Sako

  1. Wannan magana a in dubawane ga masu hankali domin al’uma suné za suyi hukunci akan wannan bayani,tunda mutane tunaninsu ya banbanta Dana shaurañ ababan halitta

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan