Yaudarar Da Ake Kira Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya – Y. Z Ya’u

  176

  Idan akwai wani abu da ke sa a zaban dan siyasa da shi, to mutanen Najeriya sun zabi shugaba Buhari ne a matsayin shugaban kasa domin ya yaki cin hanci da rashawa. Ya riga ya fahimci cewa, idan akwai abin da zai kawo shi a kan karagar mulki bai wuce yaki da cin hanci da rashawa ba. Ko a zamanin mulkinsa karo na farko a shekarar 2015, ya yi amfani da cewa zai yaki cin hanci da rashawa wanda hakan ya sa mutane suke ta faman shakkan shi, domin ya sha fadin cewa, “idan ba mu yaki cin hanci da rashawa ba, to cin hanci da rashawa zai iya kashe mu.”

  Amma a yanzu bai damu ba ko dai cin hanci da rashawa ya kashe mu ko kuma ya cire hannunsa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

  Ko ya zama al’adanmu cewa, duk lokacin da mutum yake kokarin samun shugabanci, to sai ya yi amfani da cewa zai yaki wannan dabi’a ta cin hanci da rashawa domin ya bata wannan ke kan mulki. Dukkan wadannan abubuwa ba dai-dai ba ne. Batun gaskiya shi ne, Buhari bai fahimci mene ne cin hanci da rashawa ba, shi ya sa har yanzu ya kasa yakar cin hanci da rashawa a cikin gwamnatinsa.

  Buhari ya san illolin cin hanci da rashawa, sai dai ya gaza wajen gano hanyoyin daqile lamarin cin hanci da rashawa. Ya dauka cewa, abu ne mai sauki hana mutane cin hanci da rashawa. Ya dai fahimci lamarin cin hanci da rashawa ba dai-dai ba, wannan ne ya sa yake tunanin cewa mutanen da ke kewaye da shi ba sa aikata laifukan cin hanci da rashawa, saboda ya yarda da su dari bisa dari. Wannan ne tushin rashin samun nasara da ya samu.

  A rashin fahimtarsa na cin hanci da rashawa ya sa yake kallon cin hanci da rashawa a matsayin shi ne na farko wajen yin almabazzarancin da kudade. Rashin fahimtar cin hanci da rashawa ne ya sa aka kasa shako kan lamarin ciki har da amfani da ofis da madafin iko, wanda ya sa lamarin ya zama kamar an haxarsa abun a gwamnatince. Wannan shi ya sa aka kasa dakile lamarin.

  A bisa halinsa na kirki ya sa a lokacin da zai yi nadi sai ya duba masu matsaloli da EFCC a kafafen yada labarai. Bayan akwai wasu matsalolin da ba kotu ba ce ta tabbatarwa da EFCC akwai su ba, akwai kuma matsaloli da EFCC ba ta iya ganowa ba ballantana a sanya a kafafen yada labarai.

  Buhari ba zai taba yarda da cewa abokansa suna yi wa gwamanti sata ko suna amfani da matsayinsu wajan aikata ba dai-dai ba. Wannan ne ya sa ya kasa fahimtar mutanen da ke kokarin nuna masa hanya, ba zai taba ganin laifin abokansa ba a kan duk wani rashin gaskiyar da suka aikata.

  A yau matsalolin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari shi ne, yadda abokansa wadanda ake kira da suna Cabal, suke amfani da karfin mulki da na ofis wajen aikata rashin gaskiya. Inda suke bayarwa da amsa da karfi da san kan wajen karfafa cin hanci da rashawa ko kuma yin amfani da ofis. Duk suna yin hakan ne domin suna da karfin iko sannan ba sa girmama fadar gwamnatin domin irin yadda da Buhari yake nuna musu.

  Da irin wannan lamari ya sa zai yi wahala Buhari ya iya yaki da cin hanci da rashawa, ko da kuwa yana kokarin yin hakan.
  Bari mu fara da wasu ayyuka wadanda ake tunanin ba su da mahimmanci. Ga wasu ayyuka wadanda ake ganin ba komi ba ne, amma kuma suna da mahimmancin gaske wajen samun nasara ga cin hanci da rashawa.

  Alal misalin, mutum ya mika Kaddarorinsa ga gwamnati. Mun san cewa dukiya tana da wuyar samu. Buhari ya kasa yin irin wannan aiki. Shi ya kamata ya zama zakaran gwajin dafi domin mutane su yi koyi da shi wajen yakar cin hanci da rashawa.

  A yanzu za mu iya fahimtar cewa, yaki da cin hanci da rashawa shi ne abin da ake amfani da shi wajen kama masu zabe. Ya bayyana cewa, zai kafa manyan jami’an cikin har da jihohi wadanda za su inganta harkokin gwamnatinsa, amma har yanzu ya kasa yin hakan.

  Ba za ka yi ikirarin yaki da cin hanci da rashawa har sai ka nuna misali a karan kanka. Idan Buhari ya kasa yaki da cin hanci da rashawa, to ta ya ya mutanensa wadanda ake zarginsu da amsar na goro su yi fatan yaki da cin hanci da rashawa.

  Cin hanci da rashawa ya mamaye majalisar ministocinsa wanda suke gudanar da lamacin a boye. Wasu da yawa sun fara yin aiki ba tare da sun bayyana kadarorinsu a kotu ba. Ana sa ran zai dauki kwararan matakai a kansu, sai dai bai yi hakan ba. Wannan shi ya kashe siyasarsa wanda ake sa ran da zarar an zabe shi to zai mutunta magoya bayansa, sai dai ya yi watsi da su lokacin da ya hau kan karagar mulki.

  Akwai darasi mai girma cikin siyasarsa. Lokacin aka gabatar da shi a kan a goyi bayan mutum mai mutunci, ya yi maraba da kowa da kowa wajen tafiyarsa.

  Duk da ya san cewa akwai mutanen da ake zargin su da cin hanci da rashawa bai dakatar da su ba, sai dai ma ya kara musu mukami. Ba a taba ganin an hukunta mutanen da suke jam’iyya daya wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa ba a kotu.

  Wasu sun samu nasarar daga hukun da ake yi musu na cin hanci da rashawa. Wannan ne ya nuna cewa, wasu tsirarun mutane ne aka hukuntawa a kan cin hanci da rashawa. Yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin Buhari na hukunta wasu zababbun mutane ya zama almara. Ya kasa kamanta yadda Obasanjo ya yi ya gudanar da bincike tare hukunta magoya bayansa.

  Dubi danbarwar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya yi wanda ya lamushe kudin kwangilar cire ciyawa a yankin da ya fito wand aba don matsin lamba ba da ba a za cire shi ba.

  Idan aka dauki yaki da cin hanci da rashawa na kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso yamma. Maimakon a kira mutanen da al’ummar garin da kungiyoyi wajen gudanar da bincike a kan zargin cin hanci da rashawa a kan alawus din sojoji da bacewar kayayyakin da makamai, sai ya rufe idanuwansa da kunnuwansa a kan lamarin. Duk kokarin da sojoji ke yi na kulawa da harkokin kasuwanci a cikin Jihar Borno, domin kokarin kare rayukan mutanen kasa. An bayyana cewa, mafi yawancin sojojin ana tura su wajen yaki da Boko Haram domin su mutu a can manyansu sami riba.

  Mazauna karkara da sauran al’umma sun yi korafi a kan sojojin da aka girke a yankunansu suna kwace musa dukiyoyinsu tare da cin zarafin su, amma yanzu ba a tuhumi sojojin ba a kan irin wannan badakkala. Lokuta da yawa gwamnati na bayyana cewa, za ta dauki mataki a kan badakkalan barnatar da kayyakin da ake kai wa ‘yan gudun hijira. Gwamnati ta kasa yin komai, kungiyoyin fararan hula ne ke gudanar da lamarin.

  Lokacin da gwamnan Jihar Borno, Zullum ya zargi abin da sojojin suke yi, hukumomin da ke yakar cin hanci da rashawa ba su ce komai ba, inda suka bayyana cewa, za su rufe babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, domin ‘yan ta’adda suka amfani da hanyar wajen kashe mutane masu wuce wa.

  Za a iya gane gazawar Buhari da rashin fahimta game da yaki da cin hanci da rashawa a dambarwar da ke faruwa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’oi na kasa, ASUU kan batun IPPIS.

  A gaskiya Shugaba Buhari ya gaza a akan abubuwan da ake zato a kansa wanda hakan ya zubar da daraja da mutunci da ake ganinsa da shi ganin an san shi mutum ne mai dattako mai gaskiya. Najeriya dai an gaza wajen yaki da cin hanci rashawa wanda shi ne fatan kowani dan Najeriya na gari mai son cigaban Najeriya.

  Y. Z Ya’u Babban Daraktan Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa Ta Zamani Da Cigaban Al`uma CITAD

  Turawa Abokai

  1 Sako

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan