Idan ban manta shekarar ba, ina tsammanin a wajejen 2005-2006 ne. Wani abokina ya gayyace ni zuwa taron wata ƙungiyarsu da suka kafa domin taimakawa al’majirai ta hanyar ɗinka musu sutura da raba musu sabulan wanka.
Duk da bayar da wannan gudunmawa, ƙungiyar tana nuna rashin jin daɗinta da rashin dacewar yadda iyayen yara musamman daga ƙauyuka suke tuttuɗo ƙananan yara inda wasun su ba su wuce shekaru uku da haihuwa ba, zuwa birane da sunan zuwa karatun allo. Wanda a ƙarshe suke ɓugewa da barace-barace da gararamba a tituna cikin ƙazanta, yunwa ga kuma uwa-uba rashin tarbiyya. Wani lokaci su ake amfani da su wajen tayar -da -zaune -tsaye domin biyan muradun ƴan siyasa.
Lallai a lokacin na yaba da yadda suka tashi tuƙuru wajen bayar da tasu gudunmawar wajen taimakon makarantun allon. Duk da dai daga baya na nuna musu kuskuren yin haka. Ba wai domin taimakawa masu ƙaramin ƙarfi kamar almajirai ba abin kirki ba ne. Sai dai ba komai suke yi ba sai ƙara wa Barno dawaki, wato dai ba su sani ba a fakaice suna ƙara tunzura iyayen yaran su ƙara tuttuɗo almajiran zuwa birnin na Kano daga sauran jihohi.
Domin dai mafi yawan almajiran da suke zuwa almajiranci birnin Kano ba wai ƴan asalin Kano din ba ne. Mafi yawa suna zuwa ne daga jihohin makobta, wasu daga Jihar Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kaduna, Bauchi, Gombe kai har daga Jamhuriyar Nijar.
Na bayyana musu cewar dole a zaunar da yaran nan wuri guda kuma a hana su bara domin yin karatun a gaban iyayensu sai ya fi tasiri da tura su yawon almajirancin. Domin idan ka kwatanta da yaron da yake gaban iyayensa yana zuwa makarantar boko da safe sa’annan da yamma ya yi karatun allon ko islamiyya sai ya fi su samun ingantaccen ilmin karatun Al’kur’anin ga kuma ƙarin ilmin wasu fannoni.
Na nuna wa abokin nawa cewa matsalar nan ta almajiranci ba wai aikin ƙungiyoyi irin nasu ba ne. Kuma na nusar da su cewar aikin nasu ba mai ɗorewa ba ne, ɗaukar Dala ba gammo ne. Babu yadda za a yi a ce ta hanyar bai wa yaran sabulu ko sutura zai hana su yin bara. Aiki ne na gwamnatocin jihohi tare da haɗin gwiwa da al’ummar gari.
Abin da na sani shi ne jiha ɗaya kacal a jihohi 19 na Arewa ba ta isa ta hana bara ita kaɗai ba kuma ya yi nasara. Domin mun ga yunƙurin haka inda aka kafa makarantun tsangaya a wasu garuruwa kuma abin dai bai ɗore ba.
Dole ne ko an ƙi ko an so jihohin Arewa baki ɗaya sai sun ɗauki tsari iri ɗaya kuma a lokaci guda, domin kawo gyara ga tsarin makarantun allo a Arewa.
Ga hanyoyin da na fahomtar da da su kuma na ke ganin idan an bi su za a iya kawo ƙarshen almajirancin ƙananan yara.
- Dole ne jihohin Arewa baki ɗaya ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar gwamnonin Arewa su kafa tsarin gina makarantun allo wacce za a haɗa da karantar da ilmin boko a kowace ƙaramar hukuma ta jihohinsu.
- Ka da a kafa irin waɗannan makarantu a ƙananan hukumomi da suke cikin ƙwaryar birnin jihohin nasu. Domin su suna da tsarin makarantun Islamiyya tabbatacce.
- Wajibi ne a hana ɗan wata ƙaramar hukuma zuwa wata ƙaramar hukuma ko wata jiha zuwa wata jiha. Kowa ya yi karatu a ƙaramar hukumarsa kuma makarantun jeka-ka-dawo za a yi, ba na kwana ba.
- Wajibi gwamnati ta shigo da masu unguwanni, Dagatai, Hakimai da Sarakuna kai da ma al’ummar yankin domin kula da gudanar da makarantun wajen ɗaukar nauyin malamai da sauran dawainiyar gudanar da makarantun.
- Gwamnati ta samar da wani tsarin da za a riƙa koyar da ƙananan sana’oi domin samun aikin dogaro da kai bayan yaran sun kammala makarantun allon.
- Wajibi al’ummar gari da masu hannu da shuni su tashi tuƙuru wajen kafa makarantun islamiyya daga Firamare har sakandare a yankunansu domin taimakawa ƙoƙarin gwamnati na bai wa kowa ilmin da ya dace da shi.
- Dole al’umma musamman Hausawa su sani cewar auren mata barkatai da tara yaran da mutum ba zai iya ciyarwa ba ganganci ne. Kuma yana cikin abin da yake ƙara yawaita yara masu gararamba akan tituna. Allah kuma zai tambaye su a kan kiwon da aka ba su ranar lahira.
- Bayan an cimma waɗannan ƙudurai. ƙarshe gwamnatocin Arewar su kafa doka duk inda aka ga wani yaro yana yawon bara za a hukunta iyayensa.
Matuƙar aka ɗauki wannan tsari kenan an raba makarantun allo da wata a ba wai ita ‘BARA’ a cikin al’umma. Almajirancin ƙananan yara kuwa sai dai mu gani a hotuna a rataye a gidajen adana kayan tarihi.

Ado Abdullahi, mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum, ya rubuto daga Kano