Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Kaiwa Gwamna Ganduje Ziyarar Goyon Baya

171

Kasa da mako biyu, bayan faduwar tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji, na jam’iyyar APC Abdulmumin Jibril Kofa, ya kaiwa gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar wata ziyara a fadar gwamnatin jiha.

Abdulmumin Jibril Kofa, ya bayyana hakan ne, a shafin sa na dandalin sada zamunta na Fasebuk, inda ya wallafa hoton sa da na gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A yau ke nan yayin dana kai wa mai girma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ziyara. Zamu ci gaba da bashi cikaken goyon baya, da gwamnatin mu da jamiiyar mu a jiha da kasa baki daya

Idan za’a iya tunawa dai a zaben cike gurbi daya gudana kwanaki 8 da su ka gabata, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sha kaye a hannun abokin karawar sa na jam’iyyar hamayya ta PDP Ali Datti Yako.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan