Wasu Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima A Kano Na Dab Da Angwancewa

191

A ranar Juma’a mai zuwa ne za a ɗaura auren wasu matasa masu yi wa ƙasa hidima, na Hukumar Kula da Shirin Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC, a jihar Kano, Mohammed Alhaji-Musa da Hauwa Yahaya-Bagudu a Masallacin Juma’a na Nigeria Airforce Base.

A ranar Laraba ne Shugaban NYSC a jihar Kano, Malam Ladan-Baba ya ce waɗannan matasa masu yi wa ƙasa hidima ‘Yan ‘Rukunin’ A sun sanar da shi aniyarsu ta yin aure jim kaɗan bayan kammala karɓar horo na makonni uku.

A ta bakin Shugaban na NYSC, lokacin da waɗannan matasa masu yi wa ƙasa hidima daga jihohin Nasarawa da Naija suka tuntuɓe shi game da batun auren, sai ya shawarce su da su samu iyayensu, su tattauna kuma su nemi izininsu.

“Na ce musu idan sun tuntuɓi iyayensu, sun samu amincewarsu, to lokacin ne za su sanar da Hukumar Gudanarwa ta NYSC don mu shigo ciki.

“Tun lokacin ban ƙara ji daga gare su ba, sai bayan wata shida lokacin da suka kawo min katin gayyata na ɗaurin aurensu, kuma mun yi farin ciki sosai.

“Sun ba ni labarin yadda iyayensu suka shiga al’amarin, suka kuma amince da auren, lokacin ne muka shiga ka’in da na’in don tabbatar da nasarar auren”, in ji shi.

Mista Ladan-Baba ya bayyana cewa wannan aure, wanda shi ne irinsa na farko da za a samu aure daga jihohi daban-daban a NYSC ta Kano, zai fito da maƙasudin kafa hukumar, wadda aka kafa don ƙarfafa haɗin kai a faɗin ƙasar nan.

Da yake bada labarin yadda suka fara soyayya, Mista Alhaji-Musa ya ce: “Mun haɗu ne a sansanin bada horo, a yayin aikace-aikacen ‘platoon ɗinmu’, musamman ranar da muka haɗu a lokacin aikin ‘platoon ɗinmu’ a ɗakin girki”.

Mista Alhaji-Musa, wanda ɗan asalin Afo ne daga jihar Nassarawa, ya ce ya yi matuƙar farin ciki da yadda mahaifan Hauwa suka karɓe shi lokacin da ya ziyarce su don bayyana aniyarsa.

“Tunda farko, yadda take rayuwarta ne ya birge ni, kirki da girmama mutane, abubuwan da na lura da su lokacin da muke sansani, kawai sai na ji ina son ta.

“Abu ne mai matuƙar ban-mamaki saboda ni da na so ne in yi hidimar ƙasa a Abuja, amma lokacin da takardar tafiya hidimar ƙasata ta fito, sai na ga an turo ni Kano, abinda na karɓa da zuciya ɗaya, ba tare da sanin wannan abin zai faru ba”, in ji shi.

A nata ɓangaren, Miss Yahaya-Bagudu, ‘yar ƙabilar Nupe daga jihar Naija, ta ce ta amince da Mista Alhaji-Musa ne saboda halayyarsa ta kirki da ta lura da ita a lokacin zamansu na makonni uku a sansani.

Ita ma a cewarta, ba ta yi niyyar yin hidimar ƙasa a Kano ba, tana mai cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah”, bisa samun miji da ta yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan