Kafofin yada labarai na yankin Turawa suna da dogon tarihi na yada labarai kan yadda suke tsinkayar sauran kasashen duniya. Babu laifi dan an yada labarai akan wasu kasashe na duniya, amma kuma sai ya zama matsala idan aka nuna son rai akan abinda aka yada.
Yana zama babbar matsala idan mutane suka fara yi maka wani kallo na daban akan abubuwan da ake yadawa a yau da kullum game da kai, misali harkar fim kan iya gyara dangantaka tsakanin mutane, sannan harkar fim ka iya zama katanga tsakanin mutane.
Kafin ka samu fim na Turawa a wannan lokacin da yayi adalci akan Musulmai akan matsalolinsu da kuma burikansu, yana da matukar wahala.
Ko dai kaga sun yi fim din sun bayar da labari akan abin da zai bata sunan Musulmai, ko kuma su fadi abinda zai canjawa mutane tunani game da Musulunci.
Sai dai a yayin da Musulmai ke fama da wannan kalubale a yankin na Turawa sai gashi kasar Norway ta fito da wani fitaccen fim na dogon zango wanda ake kira da ‘Series’ a turance mai suna ‘Skam’.
A wannan fim sunyi kokarin nuna kyawawan halayen Musulmai ba tare da nuna son rai ba. Fim din ya mayar da hankali akan jarumar da ta fito a matsayin Musulma mai suna Sana Bakkoush, wacce take da ilimi, kokari, rikon addini,
Fim din yana magana akan yadda Sana ta taso a wajen da mutane basu yadda da addininta ba, inda mutane suke yi mata kallo na daban akan yanayin shigarta, al’adarta da kuma yadda take mu’amala da jama’a.
Wannan fim dai yayi kaurin suna saboda abinda wannan jaruma take yi a cikin wannan fim din, saboda duka abinda yake faruwa a rayuwar Musulmi na kwarai kenan amma bama son nunawa.
Babban dalilin da ya sanya zamu iya danganta kan mu da Sana shine, duka halinmu daya Musulmai, Muna cikin rashin tsaro a rayuwarmu game da yadda duniya ke kallon mu.
A cikin irin maganganun da Sana take yi a cikin fim, ta ce: “Idan kun ji wani yana maganar batanci akan addini, kada ku saurare shi. Saboda kiyayya ba daga addini take zuwa ba, ta na zuwa daga cikin tsoro ne.”
Wannan fim dai yayi kaurin suna sosai, inda wasu kasashen na duniya suka dinga kwafar wannan fim suna yin shi da yarensu, kasashen sun hada da kasar Amurka, Italy, France, Germany, Spain da kuma kasar Denmark.
Saboda haka idan kuna bukatar fim da zai debe muku kewa ku nemi fim din ‘Skam’ ku sha kallo.
Domin cigaba da samun labarai da dumi-duminsu, ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, sannan kuma ku aika labaran mu zuwa shafukanku na sadarwa domin wasu su amfana.

