Ƙungiyar Boko Haram Ta Kusa Sharemu Daga Doron Ƙasa – Mazauna Garin Chibok

183

Mazauna garin Chibok, a jihar Barno sun koka cewa a sannu-sannu Boko Haram na gab da gamawa da mutanen garin baki dayansu.

Shugaban kungiyar mazaunan garin Chibok mai suna ‘Kibaku’ Dauda Illiya ne ya bayyana cewa a ranar 14 ga watan Janairu, 2016 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa iyayen da aka yi garkuwa da ‘ya’yansu alkawarin cewa gwamnati zata kafa kwamiti domin tsara hanyoyin da za abi domin ceto sauran ‘ya’yansu dake tsare a hannun Boko Haram.

Illiya ya ce shekaru hudu sun wuce shugaban kasa Buhari bai cika alkawarin da ya dauka ba.

Ya ce a yanzu haka babu wanda ke da masaniyar inda yaran suke ko sanin irin hobbasan da gwamnati ke yi domin ceto su tun a wancan lokaci zuwa yanzu.

Duk da cewa gwamnati na ta kurin cewa ta kusa gamawa da Boko Haram, harin da kungiyar ke kai musu bai kakkauta ba domin har yanzu suna fafurar su.

“ Ko a jajibirin kirisimetin shekarar 2019 Boko Haram sun kai hari a wani kauyen Kwarangilum dake kusa da Chibok. Sun yi garkuwa da mutane biyar, sun kona gidaje da dama sannan sun yi awon gaba da dabbobin mutane. Kwanaki biyar bayan haka Boko Haram suka far wa kauyen Mandaragrau, nan ma sun yi garkuwa da ‘yan garin Chibok guda 17.

Mazaunan garin sun yi kira ga gwamnati ta kawo musu dauki kada a wayi gari babu garin Chibok kuma a doron kasa. Domin abin da suke kokarin yi kenan.

Bayan haka sun roki gwamnati da ta karkato da akalarta zuwa wannan gari na Chibok domin hare-haren sun yi kamari matuka da idan ba a haka ba za su gama da mu karkaf.

Idan ba a manta ba a ranar 15 ga watan Afrilun 2014, Boko Haram sun yi garkuwa da daliban makarantar sakandare dake Chibok 276.

164 cikin daliban sun koma ga iyayen su sai dai sauran har yanzu ba a ko maganar su.

Premium Times

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan