NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar SSCE 2019 Ta Nuwamba/ Disamba

109

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Ƙasa, NECO ta saki sakamakon Jarrabawar Kammala Sakandire ta 2019, wato SSCE 2019 ta watannin Nuwamba/Disamba.

Abubakar Gana, Muƙaddsshin Magatakardar NECO ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis.

Mista Gana ya ce jimillar ɗalibai 70,140 suka yi rijistar jarrabawar, ɗalibai 65,207 suka zauna jarrabawar Turanci, ɗalibai 41,214 daga wannan adadi, abinda ke wakiltar kaso 63% sun samu ‘Distinction’ ko ‘Credit’.

Ya ƙara da cewa ɗalibai 66,398 sun zauna jarrabawar Lissafi, daga cikin wannan adadi, ɗalibai 54,565, abinda ke wakiltar kaso 82% sun samu ‘Distinction’ ko Credit’.

Mista Gana ya ci gaba da cewa ɗalibai 33,576, adadin da ke wakiltar kaso 48.68%, sun samu ‘Credit’ biyar zuwa sama a Turanci da Lissafi.

“A ɗaya hannun, ɗalibai 50,057, adadin da ke wakiltar kaso 72% sun samu ‘Credit’ biyar zuwa sama a Turanci ko a Lissafi.

“Gwajin haziƙar ɗalibai da suka samu ‘Credit’ biyar zuwa sama a Turanci da Lissafi a 2018 da 2019, ya nuna cewa a 2018, sun kai kaso 62.48%, a 2019 kuma, kaso 48.68%”, ya bayyana haka.

Muƙaddashin Magatakardar ya ce wannan adadi ya nuna an samu naƙasu a hazaƙar ɗalibai da kaso 13.8% a 2019.

“Wannan sakamako na zuwa ne kwana 49 daidai bayan an zana jarrabawar ƙarshe. An yi jarrabawar ne a jimillar darussa 29.

“Kamar yadda koyaushe muke nunawa, wannan jarrabawa ce da ake shirya wa ɗaliban da suke waje waɗanda ke son cika ƙa’ida mafi ƙanƙanta ta shiga makarantun gaba da sakandire”, in ji Mista Gana.

Amma Mista Gana ya lura da cewa ba dukkan ɗaliban ba ne suke neman ‘Credit’ ba a Turanci ko a Lissafi ko duka biyun.

Bisa samun ɗalibai da yin maguɗin jarrabawa a 2019 kamar yadda aka samu a 2018, Mista Gana ya ce an samu maguɗin jarrabawa sau 12,084 a 2018, a 2019 kuma, an samu maguɗin jarrabawa sau 17,004.

“Wannan ya samu ne sakamakon cikkaken sa ido da manyan ma’aikatanmu suka yi. Wannan kuma ya haifar da samun ragi a yawan ɗaliban da suka samu ‘Credit’ biyar zuwa sama”, ya ƙara da haka.

Ya yi kira ga ɗalibai da su ziyarci shafin Intanet: www.neco.gov.ng, su latsa ‘NECO Results’, don duba sakamakonsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan