Na Cika Dukkan Alkawurran Dana Ɗaukarwa Ƴan Najeriya – Muhammadu Buhari

120

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya zuwa yanzu ya cika dukkan Alkawurran da ya daukarwa al’ummar ƙasar nan game da batun tsaro tun kafin ya zo mulkin ƙasar nan a shekarar 2015.

Buhari ya fadi a hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ya ce “Na yi alkawarin kawo karshen ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram, garkuwa da mutane da sauram dukkan ayyukan ta’addanci da suka dabaibaye kasar mu Najeriya.”

Shugaban, ya kuma kara da cewa “Na san kowa zai yarda da abinda na fadi cewa nasarorin da muka samu ya dawo da girma da kuma kimar kasar mu Najeriya a idon duniya, haka kuma ina so na yi godiya ga ‘yan Najeriya bisa yarda da suka yi da gwamnatin mu.” A cewar shugaba Buhari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan