Masu Cin Beraye Sun Bayyana A Kano

109

A yayin da masana lafiya ke gargadin mu’amala da Beraye domin gujewa kamuwa da cutar Lassa sakamakon cutar an gano cewa Beraye ne ke hadda sa cutar ga bil Adama.


Sai ga shi wasu mutane da suka mayar da Beraye naman cimakar su a cikin abincin sun a yau da kulum.


Mutanen wanda suka ya da zango a cikin garin Rogo dake karamar hukumar sun ce cikin Berayen da suke ci babu wanda ya taba samun wata matsala ga lafiyar su, duk da cewa cutar Lassa ta samo asali ne ga Beraye.


Michel Joseph da shi da iyalai da ‘yan uwansa wanda suka sami masauki a cikin garin Rogo ya ce ” Mu masu kama Beraye ne kuma ba mu san irin Berayen ba kuma bamu samu matsala da sub a, domin kuwa abincin mu ne Bera muna kama su kuma muna cin su, duk cikin mu babu wani wanda ya samu wata cuta gamunan garau muna zaune har kwado muna ci”.

“Berayen da a ka ce suna kawo cutar mu a yankin mu babu wani Bera mai cutar, mu da muke ci har yanzu ba mu samu wata matsalaba, mu (27) wanda muke cin Berayen mu yi miya da su mu zuba a abincin mu har yanzu babu wata matsala da muka fuskanta”.


Yanzu in na kawo muku Bera za ku siya?


“Ba ma siya muna amfani da tarkon mu kama, ko ka kawo ma nan aka ba za mu siya ba, wanda muke kamawa shi muke ci muke kaoshi”.


Wane irin tarko ku ke amfani ku kama Berayen?
“Mun hada tarko mu saka a kan hanyar Berayen ba tare da wata matsala ba, ka gam un zo garin Rogo mun zauna mun samu abun da muke bukata yanzu muna saka tarko sai ka gam un kama Beraye da yaw aba tare da wata matsala ba, kuma mu gyara mu ci ko ciwon kai ba ma yi”.


A na baku hadin kai yayin kama Berayen?


“ Eh bamu da wata matsala domin mahukunta sun san da zaman mu kuma in zamu shiga cikin gona mu kama zamu shiga ba tare da wata matsala ba, in kuwa k ace mu fita daga gonar Raken ka sai mu fita tunda har yau ba wanda ya ce mun yi masa satar rake a cikin gonar sa”. Inji Michel Joseph a cikin tattaunawar mu da shi”.

DalaFM Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan