Yadda Nasir Yahaya Daura Ya Ke Inganta Harkar Ruwan Sha A Daura Da Kewaye

128

Ruwa aka ce shi ne ginshikin rayuwa, domin haka samar da tsabtatatcen ruwan sha ga jama’a wani nauyi ne da ya rataya a wuyan kowacce gwamnati.

A ƙokarinsa na samar da ruwan sha ga al’ummar da ya ke wakilta, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Daura, a majalisar dokokin jihar Katsina, Honarabul Nasiru Yahaya Daura, ya fara aikin gyara rijiyoyin burtsatse da su ka lalace a fadin karamar hukumar ta Daura.

Aikin gyaran rijiyoyin burtsatse da aka fara da mazaɓar Daura zai cigaba zuwa sauran mazaɓu da ke faɗin ƙaramar hukumar, inda za’a gyara rijiyoyin burtsatse sama da guda 30, tare kuma da samar da wasu sababbi.

Honarabul Nasir Yahaya Daura ya ce samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar ƙaramar hukumar Daura na daya daga cikin manyan ayyuka da zai fi bayar da fifiko a kai.

A ƙarshe ya ce zai cigaba da za ge damtse wajen bullo da shirye-shirye waɗanda za su taimaka gaya wajen magance matsalolin da ake fuskanta a ɓangaren samar da ruwan sha, da ilimi da kuma kyautata rayuwar al’ummar ƙaramar hukumar Daura.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan