Ƴan Bindiga Sun Ƙone Mutum 16 Da Ransu A Jihar Kaduna

315

Yan bindiga sun kone kimanin mutum 16 ‘yan gida daya lokacin da suka ka hari a kauyen Bakali da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne ranar Talata da misalin karfe hudu na asubahi inda suka banka wa buhunhunan hatsi da ababen hawa da babura wuta.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kulle mutanen 16 a cikin daki sannan suka banka masa wuta.

Wani mazaunin garin, Alhaji Sani Bakali, ya shaida wa jaridar cewa kimanin ‘yan bindiga 100 suka yi wa kauyen dirar mikiya

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan