Shekara 6 Da Kashe Sheikh Albani: Iyalinsa Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki

200

Shekara shida kenan cif tun lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kashe malamin addinin Musluncin nan mazaunin Zariya, Sheikh Muhammad Auwal Albani. Jaridar Dalily Trust Saturday ta ziyarci gidan mamacin ta tattauna da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa don jin halin da iyalin malamin suke ciki tun daga lokacin da aka yi kisan.
Ga fassarar tattauanawar:
Daily Trust: Ya sunanka kuma mene ne dangantakarka da marigayi Sheikh?

Abdulrahman Auwal Adam Albani: Sunana Abdurrahman Auwal Albani, ni ne ɗansa na farko, shekarata 27. An kashe shi ne tare da ɗaya daga cikin matansa da kuma ƙanina- Abdullahi Auwal. Ya bar mata uku da ‘ya’ya 22.

DT: Ya iyalin suke yi tun lokacin da aka kashe mahaifinku?

Abdulrahman: An kashe Malam ne ranar wata Juma’a a kan hanyarsa ta dawowa daga karatun dare daga makarantarsa ta Islamiyya dake Tudun Wada, tare da matarsa da wani ɗansa a cikin mota. Matarsa, Umma Abdulbari, ɗaya daga cikin ɗalibansa mai suna Bello da kaɗan daga cikin ‘ya’yansa da suka haɗa da Abdulbari, Abdulhalim, Faruk da Abdulhakam duk suna cikin motar lokacin da ‘yan bindigar suka buɗe musu wuta. A nan take aka kashe Malam, matarsa da wani ɗansa. Sun kuma harbi wasu ɗalibansa; duk da dai sun tsira. Tun da aka kashe shi, mun ci gaba da tafiyar da makarantun da ya gina don tafiyar da rayuwarmu, saboda da su muke biyan buƙatunmu da na iyayenmu. Ba abinda za mu ce sai alhamdu lilLah. Malam yana da shirin faɗaɗa da yawa daga cikin cibiyoyin ilimi da ya kafa kafin a katse rayuwarsa. Ka tambaya ko akwai wata matsala tattare da makarantun. Tabbas, akwai, amma ba za mu ce ta yi muni ba. Matsalar ita ce waye zai ɗauki ragamar shugabanci daga cikin ɗaliban Malam. Kawo yanzu, wannan shi kaɗai ne ƙalubalen da muke fuskanta a wajen tafiyar da cibiyoyin.

DT: Jami’an tsaro sun ce sun cafke mutane biyar da ake zargin su ne suka kashe marigayi Malam. Shin an tuntuɓi iyalinku don jin wasu bayanai game da waɗanda ake zargin su suka kashe shi?

Abdulrahman: Mun ji labarin ne a kafafen yaɗa labarai kamar yadda kowa ya ji. Game da tambayarka ta biyu, zan iya cewa a’a. A iya sani na, ba wanda ya gayyaci ɗaya daga cikinmu game da kama waɗanda suka kashe Malam. Kuma tun lokacin, muna ta sauraro ko za mu ji an gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu amma ba mu ji komai ba. Ta ɓangaren hukumomi, ba wanda ya zo wajenmu.
DT: Malam ya bar wasicin cibiyoyin ilimi da dama. Ya kake ganin ci gaban su?

Abdulrahman: To, suna ci gaba indai banda yadda wasu daga cikin almajiransa suke tafiyar da wasu daga cikin cibiyoyin da ya kafa tuni ko waɗanda ya so ya kafa. Misali, a ginin masallaci; kusan shekara ɗaya kenan da ginin ya tsaya. Wannan ta faru ne saboda an samu rabuwar kai tsakanin almajiransa ko dai saboda kuɗi ko saboda shugabanci. Muna da ra’ayoyi mabambanta game da yadda ake tafiyar da abubuwa. Mu ba kuɗi ne suka dame mu ba- albarkar da ake samu daga cibiyoyin ita ce ta dame mu, saboda haka muna sa baki a harkokinsu. Babu hikima ko buƙatar yin faɗa a kan kuɗi ko shugabanci. Fatanmu kaɗai shi ne duk kyawawan abubuwan da Malam ya bari su ɗore. Wannan shi ne abinda muke addu’a.

Daily Trust ta kuma tattauna da Mahmud Shu’aib Auwal, wanda ɗan uwa ne kuma ɗaya daga cikin ɗaliban Albani.

DT: Shin akwai wasu bayanai game da kamen da ake cewa an yi na waɗanda suka kashe Sheikh Albani?

Mahmoud Shu’aib Auwal: Ni ɗan ɗan uwan Malam ne kuma shi ya raine ni. Lokacin da hukumomi suka ce sun kama wasu, daraktan makarantar ya yi ƙoƙarin yin magana da su game da kamen a wancan lokaci; amma tun daga lokacin ba mu ƙara ji daga gare su ba. To ba mu sani ba waɗanda suka kashe Malam ne aka kama ko kuwa. To amma a matsayinmu na ‘yan gidan Malam, ya kamata gwamnati ta yi mana bayani game da waɗanda ake zargin. Shin tabbas su su ne waɗanda suka kashe Malam? Kuma su wane ne suka ɗauki nauyin wannan mummunan aiki, wane hukunci aka ɗauka a kan su? Waɗannan suna daga cikin wasu tambayoyi masu muhimmanci sosai da ya kamata iyalin Malam su sani.

DT: A lokacin da ka ji cewa an kama waɗanda ake zargi, shin ka yi wani ƙoƙarin ganin an hukunta su, ko kar bar komai ga Allah kamar yadda ɗan wanka ya ce?

Mahmoud: Malam, a lokacin rayuwarsa, koyaushe yakan gargaɗe mu da kada mu sake mu tayar da fitina kuma muna iya ƙoƙarinmu don mu ga mun yi haka. Mu masu son zaman lafiya ne. Koyaushe muna addu’a da fatan Allah Ya ji ƙan Malam. Ya rage gwamnati ta yi yadda ta ga dama, ba abinda za mu iya yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan