Rayuwata Zata Faɗa Cikin Haɗari Muddin Na Shiga Birnin Kano – Adam Zango

9

Jarumi Adam Zango ya bayyana cewa ya fasa zuwa Kano, domin idan aka kama shi za a wulakanta shi saboda rashin gata.

“Na fasa zuwa Kano a yau Lahadi, ba don komai ba sai don in zauna lafiya. Ina da iyali da kuma wadanda na ke taimaka mawa, idan suka kama ni za su wulakanta ni, domin ba ni da gata sai Allah”, cewar Adam A. Zango

Idan ba a manta ba dai, a jiya hukumar tace finafina ta jihar Kano, karkashin jagorancin Isma’il Na’Abba Afakallah ta bada sanarwar cewa muddin Adam A. Zango ya shigo Kano za su kama shi.

Murryar Ƴanci

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan