Buhari Ya Gaza Magance Matsalolin Cikin Gida Ina Ga Ta Kasa? – Shehu Sani

137

Tun bayan fitar wata wasika da mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a fannin tsaro, Manjo Janar Babagana Manguno mai murabus ya rubutawa shugaba Buhari, wannan lamarin ya dau sabon salo.

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani wanda yayi tsokaci akan wannan wasikar.

Rashin jituwa a tsakanin mukarraban shugaba Muhammadu Buhari ba sabuwar dambarwa ba ce, an dade ana samun irin wannan matsalar a cikin gwamnatin. Babu wanda za a daurawa laifin da ya wuce shugaba Buhari.

Domin kuwa ya gaza hada kan ma’aikatansa, a halin da kasar take ciki kuwa kamata ya yi duk wani mai aiki karkashin shugaba Buhari, ya sa tunanin kasar a gaba ba wani abun da mutum zai samu ba, don akwai bukatar kawo karshen kashe-kashe da ke abkuwa a kasar.

Wasikar da Babagana Manguno ya rubutawa shugaba Buhari, na kara jaddada cewar akwai matsala mai tsami a cikin fadar shugaban kasa.

Wannan matsalar ta cikin gida ita ce ta hana gwamnatin iya shawo kan matsalar rashin tsaro a kasa. Wasikar dai ta kunshi cewar Abba Kyari shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, yana kaka gida a harkokin kasar, duk kuwa da cewar bashi da wani hurumi da kundin tsarin mulki ya bashi.

Shehu Sani ya kara da cewa duk wannan laifin na shugaba Buhari ne, tunda kuwa ba a samu irin wannan barakarba a gwamnatocin da suka shude, hakan na da nasaba da rashin iya jagoranci nasa.

Ko a ‘yan kwanakin baya shugaba Buhari ya furta cewar babu inda nauyi ya rataya akan sa, na ya sulhunta Sarakuna da Gwamnoni, haka kuma yana kara nuna gazawar sa a wajen shuganaci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan