Gwamna Ganduje Ya Yi Ganawar Sirri Da Bola Tinubu

164

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara wajen daya daga cikin jigajigen jam’iyar APC na kasa wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidan sa dake Lagos domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi Jam’iyar APC da kuma kasa baki daya.

Wannan ganawar dai na zuwa ne kwana biyu da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci kotun kolin kasar nan da ta sake duba daftarin hukuncin da ta yanke akan kalubalantar nasarar da su ke yiwa Abdullahi Umar Ganduje, ya samu a zaben shekarar 2019.

Idan za a iya tunawa dai kotun kolin kasar nan ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Injiniya Abba Kabiru Yusuf su ka gabatar a gabanta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan