A Cikin Wata Ɗaya Aure 4000 Ne Ya Mutu A Abuja – Lauya

444

Wata lauya mai zaman kanta a Abuja mai suna Annebrafa ta bayyana cewa a yanzu haka a babban birnin tarayya Abuja tana da kesa-kesai 4000 wanda gaba dayan su akan sakin aure ne.

Aure wani abune da yake bukatar ko wanne bangare yayi aiki tukuru dan komai ya tafi yanda ya kamata,kamar yanda wadansu suke fada idan an samu zaman lafiya.

Kamar yanda a wadansu lokutan ake zabar rabuwa idan abubuwan suka ki dadi,a duk inda aka ga an samu rabuwar aure to tabbas akwai inda aka samu matsala ko kuma duka ma’auratan basu shiryawa auren ba.

A ranar Juma’a 21 ga watan Fabrairu wannan lauya mai zaman kanta a Abuja wadda aka fi sani da Annebrafa ta bayyana a shafin sada zumuntar ta na Twitter cewa tana da kesa -kesai 4000 akan rabuwar aure kuma duk a cikin wannan shekara.

Ta kara da cewa wannan lissafin iyakar na babban birnin tarayya Abuja ne ina kuma ga ragowar jihohin.

Annebrefa ta kara da cewa da yawa daga cikin wadannan aure-aure basu wuce shekara Daya ba, inda ta kare dayin tambayar “shin me yake faruwa haka”.
Ga abinda Annebrefa ta rubuta a shafin ta na Twitter.

“A babban birnin tarayya Abuja muna da kes-kes 4000 da ya shafi sha’anin rabuwar aure.

“Mafi yawa daga wadannan aure-aure basu wuce shekara daya ba, shin me yake faruwa haka?”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan