Wata Mata Ta Haife Tagwaye A Layin Karɓar Tallafin N-Power A Jigawa

128

Wata mata ta haifi tagwaye a lokacin da take kan layin karbar tallafin N-Power a kofar Fadar Hakimin Aujara Malam Aminu Danmalam.

Matar mai suna Khadija Abubakar mai shekara 35 da ke sana’ar kuli-kuli ta je amsar tallafin ne daga kauyen Gorarun inda ta haifi tagwayen maza a wajen.

Hakimin Aujara Malam Aminu Danmalam ya tabbatar da faruwar lamarin. Wata majiya ta cematar ta haihu ne lokacin da ake tantance ta, ganin haka aka kai ta wani gidan burodi da ke makwabtaka, inda a can ta sake haifar wani dan.

A jawabin shugaban shirin, Malam Bala Chamo ya ce mutum 14,000 ne suka amfana da tallafin Naira dubu biyar-biyar yayin da kuma mutum dubu dari ne za su amfana da tallafin a Jihar Jigawa. Ya ce kafin wannan rana a baya ana ba mata 65,229 amma yanzu an kara mata 34,771.

Aminiya Trust

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan