Taurin Bashi Ya Sanya Kotu Yin Umarni Da A Ƙwace Gida Da Kamfanin Buba Galadima

136

Hukumar Kula da Kadarorin Najeriya (AMCON), ta kwace gidan da tsohon makusancin Shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima ke ciki.
Ta kuma kwace ginin sa da kamfanin sa mai suna Bedko Nigeria Ltd ke ciki da kuma kamfanin gaba dayan sa.

Kwace kadarorin na Buba Galadima a yau Talata a Abuja, ya biyo bayan wani sammaci da Hukumar AMCON ta ce ta samo na iznin kwace kadarorin daga Babbar Kotun Tarayya a Abuja.

Kakakin AMCON, Jude Nwauzor ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja.

Ya ce Mai Shari’a A.I Chikere ne ya bada sammacin umarnin kwace kadarorin na Galadima.

Ya ce an kwace kadarorin ne bayan da kamfanin Buba Galadima ya kasa biyan bashin naira bilyan 900 da ake bin sa, wanda ya karba a Bankin Unity.

Ya ce an tsara yarjejeniyar biyan kudaden tun cikin 2011, amma bai biya ba.

Sai dai Buba Galadima ya karyata hukumar ta AMCON, inda ya ce bi-ta-da-kulli ne kawai ake yi masa, saboda ya matsawa Shugaba Buhari da caccaka da kuma gaskiyar da ya ke fadi.

Ya ce, “Don ka karbi kudi da nufin yin odar takin zamani a cikin 2003, ka aika ta kudin a bankin Amurka, sai aka rike kudin, jami’an Amurka suka ce su na binciken bankin da aikata wani laifi, kuma har yau ba a maido maka kudin ka ba, to mene ne laifi na.

“Da farko an kai ni kara kotu, na yi bayani, da na ga ana neman a yi min kulle-kulle, sai na daukaka kara.

“Na daukaka kara, kuma kotu ta gamsu, an kori karar. Yanzu kuma daga baya an zo ana musguna min, ana wulakanta ni saboda siyasa. To ni dai ba zan daina fadin gaskiya ba.” Inji Galadima.

Galadima yace shi ma har yanzu jiran a maido masa da kudin ya ke yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan