Wata Kotu Ta Yankewa Tsohon Kakakin PDP Zaman Shekaru 7 A Gidan Yari

121

Wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin tarayya, ta yankewa tsohon kakakin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Olisa Metuh, zaman gidan gyaran hali na tsahon shekaru 7, bisa samun sa da laifin almundahanar Naira miliyan 400.

Da yake yanke hukunci ranar Talata, alkalin kotun, Mai shari’a Okon Abang, ya ce ya kama tsohon jami’in na PDP ne da laifi guda daya – na halatta kudin haramun.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa ce ta shigar da shi kara, inda ta zarge shi da karbar kudin daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha’anin tsaro, Kanar Sambo Dasuki.

Gidan talbijin na Channels TV ya ambato Mai shari’a Abang yana cewa “Ra’ayina shi ne Metuh ya karbi N400m daga ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro ba tare da wata hujja ta kwangila ba; don haka an same shi da laifi daya na halatta kudin haramun.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan