Ƴan sandan Kasar Nan Na Bukatar Bindigogin Zamani Dubu 250 – Sifeto Janar

124

Babban Sifeton ‘Yan Sandan kasar nan Muhammad Adamu, ya ce rundunarsa na bukatar manyan bindigogi na zamani akalla dubu 250, da kuma kananan bindigogi kirar Pistol akalla dubu 100, baya ga karin zaratan jami’ai da a yanzu take fuskantar karancinsu

Muhammadu Adamu ya bayyana muhimman bukatun rundunarsa domin samun nasarar gudanar ayyukanta ne, yayin taron ganawa da jama’a da kwamitin majalisar wakilan kasar dake sa ido kan ayyukan ‘yan sanda ya shirya a Abuja.

Karin bukatun da babban Sifeton ‘yan sandan ya zayyana sun hada da baiwa rundunarsa motoci masu sulke akalla dubu 1000, da kuma gurnetin hayaki mai sa hawaye akalla miliyan 2, domin kara musu karfin gudar da ayyukansu.

Shugaban rundunar ‘yan sandan ya kuma shaidawa kwamitin majalisar wakilan kasar nan cewa akwai bukatar samar musu jirage marasa matuka akalla dari 7 da 74 da kuma na’urorin sa ido akalla dubu 1.

Bukatun rundunar ‘yan sandan kasar nan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da bangarori a ciki da wajen kasar nan ke tafka muhawara kan bukatar inganta walwala da jin dadin jami’an ‘yan sanda musamman ta fuskar hakkokinsu na albashi da kuma alawus, sai kuma bukatar kara yawansu, sama da adadinsu na kimanin dubu 305 ko kasa da hakan a halin yanzu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan