Haramta Bara Zai Amfani Al’umma – Sheikh Pantami

265

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya yi watsi da matsayar da wasu malamai suka dauka kan haramta bara da aka yi a Kano, inda ya ce haramcin alheri ne ga almajiran, iyayensu da ma al’umma baki daya.

Sakataren yada labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar, ne ya nakalto maganar da Pantami ya yi yayin da yake gabatar da mukalarsa a wajen bikin yaye daliban Kwalejin Kimiyya ta Kano, ranar Jumma’a.

“Abin da nake cewa kan maganar nan shi ne, bai dace a ce ‘yan uwana malaman addini su fito suna kalubalantar gwamnan (Ganduje) haka kawai. Yakamata su zo ne a zauna a bullo da mafita kan wannan al’amarin.

“Saboda babu makawa kai yaran nan makarantar boko ne alheri garesu, iyayensu da ma al’umma baki daya.

“Ina son ku gane, idan akwai wani abu sabo ko bako, to a samar da hanyar da za a zauna domin tattaunata sai ka yadda za a shawo kan matsalar,”inji Pantami.

Ministan ya ce, a shirye ya ke, ya kasance cikin wadanda za su tattauna kan matsalar idan an samar da kwamiti.

Ya ce, “Ina son kasance cikin wannan tattaunawa , idan aka samar da gungun mutanen da za su tattauna a kai.

“Dukanmu muna da ‘ya’ya. ‘Ya’yana na tare da ni. Ni nake ciyar da su da kai na. Kun san ciyar da yara hakkin iyayene,” inji shi.

Pantami ya ce, ya na da tabbacin Gwamnan ba zai kirkiro wani abu da zai cutar da al’umma ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan