Tsoron Kamuwa Da Cutar Corona Ya Sanya Kanawa Gudun Ƴan China

116

Yan kasar China mazauna jihar Kano sun fara nuna damuwa kan yadda mutane suke gudunsu ko nuna musu kyama kiri-kiri tun bayan rahoton bullar cutar corona.

Tun da farko dai cewa wani dan China ya shiga wani shago a kasuwa domin yin siyayya, ko da shigarsa shagon sai mutane suka fara guduwa daga inda yake.

Ko da mutumin ya bar cikin shagon ya fito waje nan ma sai mutane suka fara darewa suna ba shi hanya, wasu ma har da toshe hanci alamar tsoron daukar cutar.

Wannan ba shi ne karo na farko da ‘yan Najeriyar ke tsoron kusantar ‘yan China ba tun bayan bullar cutar coronavirus.

Sai dai wakilin ‘yan kasar Chinar a Kano ya yi kira ga jama’ar Najeriya da su rinka yin kasuwanci da ‘yan China ba tare da tsoro ko kuma fargaba ba duk da cewa cutar coronavirus ta taso daga Chinar.

Mike Zhang ya bayyana cewa sun yi taro iri daban-daban da mutanensu ‘yan China kuma sun wayar da kansu kan irin abubuwan da ya kamata su yi na kare kai.

A shekarar da ta gabata ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nada Mista Zhang a matsayin Wakilin ‘yan China inda ya ke jagorantar sama da ‘yan China 5,000.

Mista Zheng ya shafe shekaru 18 yana zama a Najeriya.

A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Kano ta fitar da lambobin ko ta kwana da za a kira idan wani na zargin bullar cutar duk da babu wani rahoto da ya tabbatar da bullar cutar a jihar.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan