Nayi Lalata Da Monica Domin Rage Nauyin Shugabanci – Bill Clinton

92

Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton yace yayi lalata da ma’aikaciyar ofishin sa Monica Lewinsky ne domin rage nauyin aikin shugaban kasa dake kan sa.

A wata hira da yayi a wani shirin talabijin da za’a fitar da shi yau, Clinton yace lalatar da yayi wadda ta kaiga yunkurin tsige shi daga mukamin sa wata hanya ce ta rage nauyin shugabancin dake kan sa, inda yace yayi takaici yadda matsalar tayi illa ga rayuwar Lewinsky.

Tsohon shugaban mai shekaru 73 yace yayi nadamar abinda yayi, ganin yadda a matsayin sa na dan adam shima ya kan yi abinda ke sa shi nadama daga bisani.

A wannan shiri na musamman da akayi na talabijin anyi hira da Clinton da uwargidan sa daban daban kan abinda suke iya tunawa a lokacin.

Mu’amala tsakanin tsohon shugaban kasa Clinton da Lewinsky ta kaiga tsige shugaban a watan Disambar shekarar 1998, kafin Majalisar Dattawa ta wanke shi a watan Fabarairun shekarar 1999.

Hillary ta bayyana mu’amalar a matsayin abinda ya dimauta ta lokacin da mijin da ya shaida mata, da kuma yadda ta bukaci shugaban ya shaidawa ‘yar su kafin maganar ta fito fili.

Clinton wanda shi ne shugaban Amurka na 42 ya nuna takaicin sa yadda batun ya mamaye rayuwar Monica Lewinsky wadda ke da shekaru 22 a lokacin.

US President Bill Clinton (R) along with First Lady Hillary Rodham Clinton award singer Aretha Franklin (C) with the 1999 National Medal of Arts and Humanities Award 29 September, 1999, at Constitution Hall in Washington, DC. (ELECTRONIC IMAGE) AFP PHOTO/Stephen JAFFE / AFP PHOTO / STEPHEN JAFFE
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan