Wani Fasto Zai Shafe Shekaru 34 A Gidan Yari Sakamakon Aikata Laifin Fyade

94

Wani fasto dan Najeriya da ya rika yi wa yara fyade ta hanyar “wankan tsarki” zai shafe shekara 34 a gidan yarin Birtaniya.


Michael Oluronbi mai shekara 60, ya ci zarafin mata shida da kuma wani yaro a tsawon shekara 20, yana mai cewa zunubi yake wanke masu.


Matarsa mai suna Juliana Oluronbi, wadda ta rika zubar da cikin da mijinta ya yi wa mata hudu, za ta shafe shekara 11 a kurkuku.

Kotun Birmingham Crown ce da ke Birtaniya ta samu mijin da matarsa da aikata laifukan.

Yayin sauraron karar, an bayyana cewa Oluronbi kan umarci mutane su yi tsirara sannan su shiga wani kwano cike da ruwa domin yi masu abin da ya kira “wankan tsarki”.


Ya yi ikirarin cewa hakan zai wanke su kuma ya kare su daga shaidan.

Sai dai mai shigar da kara Philip Bradley QC, ya fada wa kotu cewa manufar Oluronbi ita ce kawai “biyan bukatarsa ta da namiji”.


A wasu lokutan, in ji Philip, mai laifin “kan yi ta aikata fyaden, abin da ke kai wa ga mata daukar ciki da kuma zubar da shi”.


An kama Oluronbi ne a filin jirgin sama na Birmingham a watan Mayun da ya gabata, yayin da yake kokarin ficewa daga Birtaniya zuwa Najeriya.

Michael Oluronbi ya fada wa ‘yan sanda cewa “shaidan ne ya sa shi aikatawa” bayan an kama shi.
Mai Shari’a Sarah Buckingham, da take yanke hukunci, ta ce laifukan Oluronbi “lallai suna cikin fyade mafi muni ga yara da kotun ta taba saurara”.

An kama Oluronbi da laifukan fyade 15 sannan kuma an fada wa kotun cewa yana da alaka da cocin Cherubim and Seraphim da ke da asali a Najeriya.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan