Ganduje Ya Naɗa Aminu Ado A Matsayin Sabon Sarkin Kano

125

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sunan Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.

Sanarwar hakan na ƙunshe ne a takardar da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya sanya wa hannu.

Dalilai Biyar Da Suka Sanya Ganduje Ya Tumbuƙe Sarki Muhammadu Sanusi II

Idan za a iya tunawa dai a yau ne Majalisar Zartarwar ta Jihar Kano ta tumɓuke Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin watsa labarai, Salihu Tanko ya wallafa ta ce Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da a sauke sarkin saboda rashin biyayya.

Sakataren gwamnatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce an sauke sarkin Kano ne saboda nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan