El-Rufa’i Ya Ba Sanusi Muƙami Kwana 1 Bayan Tumɓuke Shi Daga Sarauta

13

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano da aka tumɓuke jiya muƙami a Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Jihar Kaduna, KADIPA.

Wata sanarwa daga Fadar Gwamnatin Kaduna ta Sir Kashim Ibrahim ta ce: “naɗin yana daga ɓangaren sake gina hukumar gudanarwa ta KADIPA, wadda doka ta yi tanadin cewa Mataimakin Gwamna ne zai jagorance ta, kuma tana da sauran mambobin cikin gida da sauran jami’an Gwamnatin Jihar Kaduna”.

Sanarwar, wadda Muyiwa Adekeye, mai bada shawara kan kafafen watsa labarai da sadarwa ya sanya wa hannu ranar Talata ta ce: “Gwamnatin Jihar Kaduna tana fatan amfana da tarihinsa, gogewa, basira da sanayya ta Maimartaba Muhammad Sanusi II, wanda kafin ya zama Sarki, ya samu kyakkyawan yabo a da’irar hada-hadar kuɗi a duniya.

“Malam Nasir El-Rufa’i ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta samu kima ta hanyar iya neman gudunmawar irin wannan mutumin don samun ci gaba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan