Na Kafa Tarihi A Masarautar Kano- Ganduje

94

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya kafa tarihi ta hanyar naɗa ‘yan uwa biyu masu uba ɗaya, Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano da Sarkin Bichi.

Gwamna Ganduje ya yi wannan furuci ne yayin miƙa takardun kama aiki ga sabbin sarakunan a ɗakin taro na Coronation Hall, dake Fadar Gwamnatin Jihar Kano.

“Wannan shi ne karon farko a Najeriya ko ma a ko’ina a Afirka inda ‘yan uwa biyu suke karɓar takardun kama aiki a matsayin sarakuna masu daraja ta ɗaya a jiha ɗaya. Haƙiƙa sun gaji kyakkyawan aikin mahaifinsu, Alhaji Ado Bayero, wanda ya yi sarauta tsawo shekara 53”, in ji shi.

A jawabinsa, sabon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya ce buƙatar mahaifinsa, Ado Bayero ta biya bisa naɗinsa da na ɗan uwansa a matsayin sarakuna masu daraja ta ɗaya.

Sarki Bayero ya kuma yi alƙawarin zama mai girmama jama’a, mai biyayya da ɗa’a kamar yadda marigayi mahaifinsu ya koya musu.

“Mun amince da hukuncin Ubangiji, mun yi imani cewa komai yana da ƙaddara da lokaci, kuma yau ga shi ya faru.

“Ina tunawa mahaifina ya umarce mu da mu rungumi haƙuri, biyayya ga hukumomi kuma mu dogara da Allah a kan komai.

“Ya kuma faɗa mana da mu riƙa yin adalci ga jama’a don mu ma Allah Ya yi mana adalci a gobe Kiyama.

“A wannan rana mai ɗimbin tarihi, zan ce burin mahaifinmu marigayi sun cika”.

A nasa jawabin, Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta samar ayyukan yi ga ɗimbin matasan da ba su da aiki yi a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan