Sauke Sanusi: Ƙungiya Ta Buƙaci Muhuyi Ya Sabunta Binciken Faifan Dala Kan Ganduje

85

Wata ƙungiya mai suna Kano Concerned for Prudent Leadership ta buƙaci Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, PCACC, da ta fara sabon bincike a kan faya-fayan bidiyo da aka ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana sunƙuma dalolin Amurka a aljihun babbar rigarsa.

A wata wasiƙa da ta aika wa shugaban PCACC, Muhuyi Magaji, wadda wani Mukhtar Sani Mandawari ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta yi kira ga hukumar da ta yi amfani da ikon da doka ta ba ta yi cikakken bincike a wannan al’amari.

“Sanin kowa ne cewa an ga faya-fayan bidiyo da dama da suka bazu a Intanet waɗanda suke nuna Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yana karɓar Dalar Amurka kuma yana murmushi, abinda ake zaton toshiyar baki ce daga ‘yan kwangila.

“Wannan ƙungiya tana yin kira ga kyakkyawan ofishinka da ka yi amfani da ikonka dake ƙarƙashin tanade-tanaden dokarka ka yi cikakken bincike a al’amarin. Wani abin farin ciki, tuni Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta tabbatar da sahihancin faya-fayan bidiyon.

“Yallaɓai, muna sane da cewa bisa Kundin Tsarin Mulki, ba za a iya gurfanar da gwamna a kotu ba saboda yana da kariya ta wucin gadi a lokacin da yake kan mulki. Amma, ba a hana hukumarka ta bincike shi ba, kuma ta fitar da sakamakon bincike.

“EFCC ta yi haka a kan Ayodele Fayose, tsohon gwamnan Ekiti, wanda ba a iya iya gurfanar da shi gaban kotu ba lokacin da yake kan mulki bisa zargin aikata laifukan cin hanci, amma ta yi bincike sosai.

“Muna fata hukumarka za ta fara bincike a kan wannan al’amari da ya damu mutane, saboda wannan al’amari ne da bai kamata a manta da shi ba”, a cewar wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 9 ga Maris, 2020.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Oktoba, 2018, Jaafar Jaafar, ɗan jarida mawallafin jaridar Dalily Nigerian ya saki jerin wasu faya-fayan bidiyo, waɗanda suka nuna Gwamna Ganduje yana karɓar dalolin Amurka.

A wancan lokaci, Mista Jaafar ya yi zargin cewa Gwamna Ganduje yana karɓar waɗannan dammmen kuɗaɗe ne waɗanda ya ce sun kai dala miliyan $5 a matsayin toshiyar baki daga ‘yan kwangilar dake ayyuka daban-daban a jihar Kano.

Majiyarmu ta Kano Focus ta ce duk da yake BBC, Premium Times da Amnesty International sun tabbatar da sahihancin faya-fayan bidiyon, amma Gwamna Ganduje ya yi watsi da su a matsayin “waɗanda aka ƙirƙira”.

Gwamnan ya kuma shigar da ƙara a kan Mista Jaafar, inda ya buƙaci ya ba shi biliyan N3, bayan da ya garzaya Babbar Kotun Jihar Kano don ta dakatar da Majalisar Dokokin Jihar Kano bincikar sa.

Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya ce hukumar tana bincike a kan waɗannan faya-fayan bidiyo.

Amma dai har yanzu EFCC ba ta saki rahoton binciken da ta ce tana yi ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan