APC Ta Buƙaci El-rufai Da Ya Ƙirƙirowa Tsohon Sarkin Kano Masarauta A Kaduna

97

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta fito ta yi magana game da huldar da ke tsakanin gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da kuma tsohon Sarkin Muhammadu Sanusi II.

Jam’iyyar ta yi wannan kiran ga gwamnan Nasir El-Rufai ya kirkiro wata sabuwar masarauta ya kuma ba tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II rikonta.

Tun da farko dai jam’iyyar APC magantu ne ta bakin mataimakinta Shehu Maigari, bayan ganin yadda gwamnan na Kaduna ya rika nuna goyon bayansa ga tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II.

A makon da ya gabata Gwamna El-Rufai ya nada tsohon Sarkin a matsayin Shugaban jami’ar KASU, hakan na zuwa ne bayan ya nada shi cikin majalisar hukumar KADIP.

“Mai girma Gwamna Nasir El-Rufai, wannan mutum ne wanda ya yi aiki domin hana APC, jam’iyyarka samun nasara, ya fito fili ya na sukar gwaninka Shugaban kasa.”

Jawabin ya kara da cewa: “Ba tare da wata hujja ko dalili mai gamsarwa ba. Amma ka zabi ka rika daukarsa wani Gwarzo.” A karshe Jigon na APC ya ba gwamnan shawara.

“Ran ka ya dade, jam’iyyar APC ta na ba ka shawarar ka kirkiri sabuwar masarauta a jihar Kaduna, wanda watakila za ta yi iko daga kasar Rigachikun zuwa Kasuwar Magani.”

“Sai ka nada Gwaninka a kan sarautar, yadda zai yi wa jam’iyyarsa ta PDP da kyau aiki a can, a maimakon ka rika ba shi wasu mukaman je-ka-na-yi-ka.” Inji Alhaji Shehu Maigari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan