An Hana Shigowa Daga China Da Amurka Da Birtaniya Cikin Ƙasar Nan Saboda Coronavirus

71

Gwamnatin tarayyar ƙasar nan ta hana baki shigowa daga China da Italy da Amurka da Birtaniya da Iran da ma wasu kasashen da coronavirus ta yi kamari.

Hukumar hana kare yaduwar cututtuka ta kasar ce ta sanar da hakan a ranar Laraba a shafinta Twitter.

Sauran kasashen da Najeriyar ta hana baki shiga cikinta sun hada Koriya Ta Kudu da Spaniya da Faransa da Jamus da Norway da Netherlands da kuma Switzerland.

NCDC ta ce akwai masu dauke da cutar fiye da 1,000 a kowacce daga cikin kasashen nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan