Coronavirus: Saudiyya Ta Hana Salla A Dukkan Masallatai

136

A ranar Talata ne Majalisar Manyan Malamai a Saudiyya ta ɗauki matakin dakatar da sallolin jam’i da ma Sallar Juma’a a dukkan masallatan ƙasar, in ji jaridar Saudi Gazette.

Sai dai wannan dakatarwa ba ta shafi Masallatai Masu Alfarma na Makka da Madina ba, Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya bada rahoton haka ranar Talata, kamar yadda ya jiyo sanarwar Majalisar Malaman tana cewa.

“Taron gaggawa na Majalisar Manyan Malaman Saudiyya Karo na 25 da aka yi a Riyad ya yanke cewa za a rufe dukkan masallatai na wucin gadi, amma za a ci gaba da yin kiran salla kamar yadda aka saba”, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan