Coronavirus: WAEC Ta Ɗaga Jarrabawarta Har Illa Ma Sha Allahu

189

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC, ta dakatar da Jarrabawar Kammala Sakandire ta 2020, WASSCE 2020 har sai illa ma sha Allahu.

Hukumar shirya jarrabawar ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

A cikin sanarwar, Patrick Areghan, Shugaban WAEC na Najeriya ya ce an dakatar da fara jarrabawar da da aka yi shirya farawa ranar 6 ga Afrilu ne sakamakon annobar Coronavirus.

Mista Areghan ya ce za a sake duba jadawalin jarrabawar bayan an samu ci gaba a annobar Coronavirus.

“Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma a Najeriya, ko kuma a nahiyar Afirka, ta yanke shawarar dakatar da Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma ga Ɗaliban Sakandire ta 2020, wadda da aka shirya farawa ranar 6 ga Afrilu, 2020”, in ji sanarwar.

“Wannan ya faru ne sakamakon tasirin annobar Coronavirus (COVID-19) da kuma irin mummunan tasirin da take da shi a wajen gudanar da WASSCE ga ɗaliban sakandire, 2020 da kuma halin ɗar-ɗar da ta jawo a tsakanin al’umma.

“Wannan mataki ya nuna irin damuwar hukumar da tallafi da take bayarwa ga irin matakai da yawa da Gwamnatin Tarayya da na jihohi na Najeriya da kuma wasu gwamnatocin mambobin ƙasashe wajen daƙile yaɗuwar cutar.

Cutar, wadda ta ta kama mutane 250,000 a faɗin duniya ta sa an soke shirye-shirye da dama a faɗin duniya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan