Tom Brady Ya Koma Sabuwar Kungiyar Kwallon Zari-ruga

24

Tom Brady dan wasan zari-ruga ne mai hazaka kuma mai nasarori a gasar da kungiyarsa daya baro yake samu ta New England Patriots.

Brady dai ya kwashe shekaru har guda 20 a kungiyar kwallon zari-ruga ta New England Patriots inda ya lashe kofuna da dama sannan kuma ya kafa manyan tarihi a tsohuwar kungiyar daya baro.

Yanzu kuwa Tom Brady ya koma kungiyar kwallon zari-ruga ta Tampa Bay Buccaneers inda itama babbar kungiyar kwallon zari-ruga ce a duniya.

Tom Brady dai ya bayyana cewar ya kamata ya tafi sata kungiyar domin gwada sa’arsa tunda har yanzu wasan na zari-ruga yanayi dashi sosai da sosai kuma ya bayyana jin dadinsa a sabuwar kungiyar kwallon zari-rugar daya koma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan