Yadda Talakawan Najeriya Su Ka Amfana Da Naira Biliyan 52 A Dalilin Coronavirus

279

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rabawa talakawan Najeriya da ke wani yanki a Abuja naira biliyan hamsin da biyu (N52,000,000,000) a cikin kwanaki biyu.

Tun a cikin shekarar 2016 gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin ga masu karamin karfi, amma saboda coronavirus, shugaban kasa ya bukaci a ninka wa mutane kudaden zuwa N20,000 maimakon dubu biyar, saboda mutane su samu saukin radadin halin da aka shiga.

Ta kuma ce gidaje sama da dubu biyar ne za a bi ana rabawa mutane kudaden a yankin karamar hukumar Kwali a Abuja

Ministar Ma’aikatar Agaji da Ci Gaban Al’umma, Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa suna bayar da kudin ne ga masu karamin karfi da suka da hada marayu da masu bukata ta musamman da mata marasa karfi da kuma wadanda mazajensu suka mutu.

Gwamnatin ta ce tana bada kudin ne domin rage radadin rashi da wasu ‘yan kasar ke fama da shi, a wani mataki na yaki da talauci a fadin kasar baki daya musamman wannan lokaci na coronavirus.

Turawa Abokai

5 Sako

  1. Kai jama’ah wai me shuwagabanninmu sunka daukemu ne? Sai rade race kaketaji a social media cewa gwabnatin tarayya ta rabawa talakkawan nijeriya sama da naira biliyan hamsin a Instagram mah masha cin karo da posting din lay Muhammad inda yaketa qaryar cewa sun rabawa talakkawan qasa kusan biliyan Dari to wlh mu bamu yadda da hakanbah don bamu gani aqasaba duk qaryar banzace wlh sundai rabewa kawunansu kawai

  2. Shugabanin Nigeria sun mayar da talakawa kamar karnukan farauta kullin karyarsu talaka alhalin sun jahiltar dashi sun talautar dashi sun jefashi cikin kangin bauta to kutuna Allah don baya bacci. Allah ya isa bamu yafeba.

  3. Allah ya isa kuma wlh kusani ce wa Allah ya nan a madakata kuma duk abida kukai abin kididdige wane wajan Allah koda ko Dan posting din labaran nan ne da kuke ku fadi gaskiya, kuma ku shuwa gaban nin Nigeria Dan Allah mu bamuce sai an bamu kudi ba dole no , in ba’a ba muba kuma Mai na azo ai mana karya wlh wlh Allah bazai taba barin hakkin wani a wajan waniba , kuma akwai hisabi wlh. Kuma daga karshe Allah ya isar mana.

  4. Aslm sunana Nafisa Muhammad Daga kaduna kawo Hayin naiya wlh a anguwanmu Akoi Wayanda zasu kwana sutashi basuciba Ga Kananan yara abun taysayi suyaka mata a tausayawa Dan Allah Ina rokan gwamnati da ta taimakawa wannan mutanen ga numbar na 08035943397

  5. Ai a gaskiya ban taba sa rai da samun wani taimako daga shugabannin Nigeria zuwa hannun talaka ba, domin wai Hausawa suna cewa an dade ana ruwa ƙasa tana shanyewa. Sai nake ganin cewa duk wanda ya kwallafa ransa akan sai Nigeria ta bashi mafita to tabbas wannan tunanin nasa zamu iya cewa zuciyarsa ta yaudare shi. Amma duk da haka muna yiwa shugabannin namu addu’a Allah ya shirya mana su sannan ya ganar dasu damu gaskiya baki daya.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan