Jihar Kano Tana Tsananin Buƙatar Tallafin Kuɗi Daga Gwamnatin Tarayya – Kabiru Rurum

163

Dan majalisar tarayya Mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana bukatar hakan a babban birnin tarayya Abuja, lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Yace daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ya kamata ta yi,shi ne ba da tallafin kayan abinci da kayan masarufi domin ragewa al’umma halin radadin da ake ciki sakamakon hana zirga zirga, saboda gudun yaduwar cutuwar corona virus .

Honourable Kabiru Alhassan Rurum ya ƙara da cewa yanayin yadda adadin masu dauke da cutar ke karuwa a jihar Kano, da Kuma karuwar mace macen alumma a ƴan kwanakin nan abin tayar da hankali ne, dan haka ya zama wajibi a hada hannu wuri guda.

Dan majalisar tarayyar ya Kuma yabawa kokarin Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje wajen yin duk mai yiwuwa domin ganin an hada yaduwar cutar a Kano.

Kabiru Alhassan Rurum Wanda tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano ne, ya Kuma bukaci al’ummar jihar Kano da su cigaba da gudanar da adduoi, donmi magance cutar corona da ta addabi Duniya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan