Ibrahim Hassan Hadejia, Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa ya ce azumi, zafi da rashin lafiya suna daga cikin dalilan mace-macen da ake samu a jihar.
An samu rahotonnin dake cewa gomman mutane sun yi mutuwar ban-mamaki a Hadejia a cikin kwana huɗu, inda wasu suke dangantaka mace-macen da COVID-19.
Sai dai a wata tattaunawa da jaridar Vanguard, Sanatan ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya gano “mace-mace 46 ne kawai”, kuma babu hujjar cewa COVID-19 ce ta kashe su.
Ya ce dukkan waɗanda suka mutu kwanan nan tsofaffi ne waɗanda dama ba su da lafiya, yana mai ƙarawa da cewa duk da an faɗa musu kar su yi azumi, amma sai da suka yi.
“Wani kwamiti mai mambobi biyar wanda yake da mamban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya gano mace-mace 46 ne kawai a Jigawa. Gwamna ne ya kafa wannan kwamiti a lokacin da ya ji labarin. Kwamitin ya je Hadejia, yana neman gaskiyar mutane 100 da ake cewa sun mutu”, in ji Mista Hadejia.
“Sun yi binciken gano dalilan mace-macen da baki. Ka san idan wani ya mutu, mutanenmu sukan binne shi da wuri. To ‘yan kwamitin sun tambayi ‘yan uwan waɗanda suka mutun, idan akwai wani zato mai ƙarfi, sukan yi musu gwaji. A yanzu, dukkan gwaje-gwajen da aka yi wa makusantan mamatan da suka haɗa da ‘ya’ya da matansu, wajen gwaji fiye da 70, duk sun nuna ba sa ɗauke da cutar.
“Hakan yana nuna abubuwa da yawa. A yanzu akwai matsalar zazzaɓin cizon sauro kuma a Hadejia, yanayin zafi a can ya wuce iyaka, digiri 241, kuma mutanenmu duk azumi suke yi. Dukkan mutanen da aka bada rahoton sun mutu tsofaffi ne da ba su da lafiya. Ko ka ce musu kar su yi azumi, ba za su yarda ba”, in ji Mista Hadejia.
“Azumi, zafi da suka haɗu da rashin lafiya su suka shafi tsofaffin suka mutu”, in ji Mista Hadejia.
Sanatan ya ce matakan da gwamnatin jihar Jigawa ta ɗauka za su daƙile yaɗuwar cutar.
Kawo yanzu, mutum 38 ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Jigawa.